Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan Nunawa Saurez Ni Ba Kanwar Lasa Bane


Manchester United's Patrice Evra (L) challenges Aston Villa's Christian Benteke during their English Premier League soccer match at Old Trafford in Manchester, northern England, April 22, 2013.
Manchester United's Patrice Evra (L) challenges Aston Villa's Christian Benteke during their English Premier League soccer match at Old Trafford in Manchester, northern England, April 22, 2013.

Juventus ta yi kunan doki 1-1 da Real Madrid, a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai wanda hakan zai bata damar buga wasan karshe.

Kungiyar ta Juventus zata yin karon batta da kungiyar Barcelona, a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, da za’a buga a 6 ga wata mai zuwa a Berlin ta kasar Jamus.

Dan wasan baya na Juventus, wato Patrice Evra, yace zai sake haduwa da Luis Suarez, kuma zai nuna masa cewa shi ba kauwar lasa bane.

A shekara 2011, lokacin da suke kungiyoyin Liverpool da Manchester United, Suarez, ya yiwa Evra, zagi na nuna bambancin launin fata wanda hakan ya jawo aka cin tarar Suarez da kuma dakatarwa daga buga wasanin 8.

Evra, yace duk wannan ba komai bane, ni dai ina alfahari da launin fata na kuma zamu yin hannu dashi amma zan taka masa leda yadda ya kamata.

XS
SM
MD
LG