Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Marcelo Ya Kare Carlos Da Ronaldo


Carlo Ancelotti
Carlo Ancelotti

Dan wasan Real Madrid mai tsaron baya Marcelo, ya kare mai horar da su, Carlos Ancelotti da dan wasan gaba Cristiano Ronaldo bayan da aka fitar da klub din daga gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

Bugun penarti da Ronaldo ya samu ya kusa sa kungiyar ta Real Madrid a hanyar zuwa wasan karshe da za a yi a Berlin.

Sai dai kungiyar Juventus ta jajirce inda ta lashe wasan da ci 3-2 idan aka yi jummalar kwallayen da kungiyoyin biyu suka zira a duk wasannin, inda tsohon dan wasan Real Madrid Alvaro Morata ya zira kwallon karshe da ta baiwa Juventus nasara.

A duk lokacin da Real ta sha kashi a wasannin ta, Ronaldo na daga cikin ‘yan wasan da ke fuskantar suka, amma a cewar Marcelo hakan bai dace ba.

A kafar sada zumuntar kungiyar ta twitter Marcelo ya ce “babu akasi a irin haskawar da Ronaldo ya ke yi, an saba ganin shi yana zira kwallaye uku zuwa hudu a wasa guda, idan kuma ya zira kwallo guda sai a ce haskawarsa ta dishe, lallai Ronaldo injin ne, yana iya bakin kokarinsa ya ga cewa ya taimakawa kungiyar, ba daidai ba ne a ce baya ya haskawa.”

XS
SM
MD
LG