Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamun Flying Eagle Ta Shirya Cin Kofin FIFA 2015


Kungiyar 'yan wasan Najeriya masu shekaru kasa da ashirin Flying Eagles,a shirye shiryen ta na karshe na shiga wasan gasar cin kofin FIFA na duniya na shekarar 2015 a New Zealand, ta doke ‘yan wasan kasa da shekaru 23 na Hoffenheim’s da ci 5 – 2 a wasan sada zumuncin da aka buga jiya ranar talata.

Wasan shine na farko a cikin jerin wassanni uku na gwaji domin shirya tawagar zuwa gasar da za’a fara daga baya a wannan watan.

Dan wasan Hoffenheims Ahmed Sassi shine ya fara jefa kwallo a raga amma sai ta bugi karfen gola ta dawo yayin da shi ma dan wasan Najeriya Chidera Eze ya kasa jefa kwallo lokacin da daga shi sai mai tsaron gida Ricco Cymer mai buga wa Hoffeinheims.

Godwin Savior dan wasan da ke bugawa Plateau United ne ya fara jefa kwallo ma Najeriya, amma kuma Allensandro Abrussia ya rama ma kungiyar su cinkin dan lokaci kadan.

Eze ya gyara kuskuren sa na farko yayin da ya sa Najeriya a gaba kafin suka sake yin kunnen doki a kokarin da Ahmed Azaouagh yayi na jefa kwallo guda.

Taiwo awo dan wasan na super eagles ne ya ba kulob din na super eagles damar lashe wasan yayin da jefa kwallaye uku, yayin da wasan ya tashi a 5 – 2.

XS
SM
MD
LG