Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Shari'ar Amurka Ta Kama Leigh Winner Da Laifin Bada Asirin Gwamnati


Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta kama wata ma'aikaciyar gwamnati ta wucin gadi kan zargin ta baiwa wata kafar yada labarai ta internet bayanan sirrin gwamnati.

Jiya Litinin ne gwamnati ta bada sanarwar hakan, a kuma dai dai lokacinda wata kafar yada labarai a Internet da ake kira Intercept, ta buga wani labari da ya nuna sashen leken asiri na sojojin Rasha yayi kokarin yin kutse cikin kundin sunayen masu jefa kuri'a na Amurka, kamin babban zaben da aka yi bara.

Wannan labari yana kunshe ne cikin bayanai da gwamnati ta ayyana a zaman sirri.

Wata takardar shaida ko ta rantsuwa da FBI ta gabatarwa kotu, tace ma'aikaciyar mai suna Reality Leigh Winner, ta amsa cewa tayi k\wafin bayanan sirri na gwamnati ta aikawa wata kafar yada labarai.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG