Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Yayi Garkuwa Da Mahaifinsa Domin Amsar Kudin Fansa


Rundunar ‘yan Sandan jihar Oyo, ta cafke wani matashi mai shekaru ashiri (20) da haihuwa Ibrahim Babatunde, tana kuma tuhumarsa da shirya sace mahaifinsa domin amsar kudin fansa.

Babatunde, ya hada baki da wasu abokansa mutane uku, Babuga Salihu shekaru ashirin (20), Aura Sands, shekaru ashirin (20), da Amuda Yusuf mai shekaru goma sha tara (19).

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Abiodun Odude, yace an sace Aliyu Babatunde, a garin Igboora kuma sai da ya kwashe kwanaki uku a hannun su kafin iyalinsa su biya Naira miliya guda ga wadanda suka yi garkuwa dashi.

Ibrahim Babatunde, yace ya yanke shawarar yin hakan ne bayan da mahifinsa Aliyu Babatunde, ya juya wa ‘ya’yansa baya inda ya daina kula dasu ya barsu su lura da kansu saboda yana da mata da yawa saboda haka sai na yanke hukunci cewa idan muka sace shi zamu sami kudi

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG