Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Yanke Mazakutarsa


Wani matashi mai shekaru goma sha shida ya yanke mazakutarsa har kuma ya kusa ya kashe mahaifiyarsa bayan da ya sha tabar we-we.

Matashi ya kwanta da wuka baya ya sha tabar ta we-we sai ya fara samun tabin hankali inda ta kai shi ga tunanin cewa akwai mutane a cikin bango dakinsa, sai ya tashi a cikin tsakiyar dare ya soka wa mahaifiyarsa wuka ya kuma yanke mazakutarsa.

Mahaifinsa ya ce dansa ya bi wasu abokai ne inda daga bisani ya tsunduma cikin shan tabar ta we-we.

Bayan da ya sha tabar ta we-we ta gayamasa karya sai ya sami dan tabin hankali da ta haifar da mummunar illa gareshi da mahaifiyarsa wace ta haifar da aikata aika aikan in ji mahaifinsa .

Likitan da ya dubashi ya ce nan gaba kadan za a sake yi masa yiyata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG