Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Ya Yiwa 'Yar Shekara 8 Fyade


An gurfanar da wani matashi Samuel David, mai shekaru ashirin da biyu da haihuwa wanda ake zargi, da yiwa ‘yar makwabcinsa mai shekaru takwas fyade.

David, mazaunin gida mai lamba 30, layin Oremeji dake Bariga a birnin Lagos, ana zarginsa ne da laifin yin fyade wanda ya aikata a ranar 12, ga watan Mayu, a gidan da yake in ji mai gabatar da kara Sajen ‘yan Sanda Raphael Donny.

Ya kara da cewa matashin ya yaudari yarinya ce zuiwa dakin sa baya ya yi mata fyade ya share mata jiki ya kuma ce mata kada ta gayawa kowa.

Baya kwana biyu sai yarinyar ta fara samun ‘yan matsaloli abinda yasa ta fadawa mahaifiyarta daga bisani ta kai rahoto ga ‘yan Sanda aka zo akayi awon gaba dashi.

Koda yake David ya musanta zargin mai shara’a Davies Abegunde, ta bada belinsa akan kudi Naira miliyan daya (1,000,000) da kuma mutane biyu da zasu tsaya masa zai kuma ajiye tsabar kudi Naira dubu dari (100,000) a kotu in ji mai shara’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG