Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Tabbata Barack Obama Ya Mallaki Gida A Gundumar Kwalambiya


Tsohon Shugaban kasar Amurka Obama da Mai dakin shi Michelle Obama.
Tsohon Shugaban kasar Amurka Obama da Mai dakin shi Michelle Obama.

Rahotanni na kara jaddada cewar tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama, zai cigaba da zama a babban birnin tarayyar kasar Washington DC, ganin yadda Obama, ya biya kudin gidan da yake haya daya kai dallar Amurka milliyan takwas da dugo daya $8.1M, kimanin naira billiyan uku.

Obama da maidakin shi Michelle Obama, sun tsara zama a Gundumar Kwalambiyar, bayan kawowar karshen zaman su a fadar shugaban kasar, a watannin baya, bisa dalilin ‘yar su Sasha, dake makaranta a babban birnin.

Hakan zai ba ‘yar tasu dammar kammala karatunta batare da wata matsala ba. A cewar mai magana da yawun Obama, Kevin Lewis, shugaban ya yanke shawarar biyan kudin gidan ne, don ganin yadda yake biyan kudin haya.

Yaga cewar gara ya biya kudin gidan, daya cigaba da biyan haya, bayan zai zauna a gidan na tsawon lokaci. Gidan dai nada dakunkuna 8, da bayi 9, yana wata babbar anguwa mai suna ‘Kalorama’ da sai wane da wane ke iya zama, kimanin tafiyar kilomita 3 daga fadar shugaban kasar ‘White House’

Gidan tsohon shugaban Obana, yana kusa da gidan ‘yar shugaban kasa Donald Trump, Ivanka Trump da mijinta Jared Kushner. Anguwar dai nada tarinhin tsofaffin shugabannin kasar Amurka biyu sun taba zama Woodrow Wilson da Willam Howard Taft.

Tun bayan barin shi karagar mulki, ya tafi hutu a kasashen Faransa da Italiya. Yanzu haka dai ya rattaba hannu a wata kwantiraki da kamfanin 'Penguin Random House' masu wallafa kasidu, don su rubuta tarihin rayuwar shi da na mai dakin shi. An kiyasta kudin littafin idan ya fito, zai kai kimanin dallar Amurka milliyan sittin $60M,

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG