Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Instagram' Da 'Snapchat' Suna Shafar Lafiyar Kwakwalwar Matasa


'Yan Mata Da Shafin Yanar Gizo
'Yan Mata Da Shafin Yanar Gizo

Bincike ya tabbatar da cewar shafufukan Instagram da Snapchat, sune shafufuka mafi koma baya ga lafiyar matasa. Shi kuwa shafin Youtube, yana taimaka ma kwakwalwar matasa.

Sakamakon binciken da hukumar ‘British Royal Society for Public Health’ suka fitar, yana nuni da cewar, yawan amfani da wadannan shafufukan da matasa kanyi yana shafar lafiyar kwakwalwar su.

An dai tabbatar da cewar shafufukan yanar gizo, suna shiga rayuwar jama'a fiye da yadda masu shan taba sigari suke kamuwa ita, ko masu shan barasa. A wannan zamanin yadda matasa suka shaku da shafufukan yanar gizo, abun ba’a ko cewa komai.

Idan za’ayi maganar lafiyar matasa a wannan karnin, sai an duba yadda suke mu’amala da shafufukan su na yanar gizo. A cewar Shirley Cramer, abun da ban mamaki, yadda aka jera shafufukan Instagram, da Snapchat, a matsayin shafufuka da suke shafar lafiyar kwakwalwa da jikin na matasa.

Masanan dai sun gwada matasa 1,500 masu shekaru 14 zuwa 24, a kasar Birtaniya, inda suka tambaye su yadda suke mu’amala da shafufukan, da kuma duba ga irin tashin hankalin da matasa kanshiga, halin bakin ciki, da irin baccin da suke yi a duk dare, halin damuwa, da dai duk wasu abubuwa da kan shafi lafiya mutun.

Binciken dai ya bayyanar da cewar, shafin Youtube shi ya zamo na daya mafi kyau ga lafiyar matasa, wanda ya biyo mishi shine Twitter, kana Facebook, instagram da snapchat na biye.

Shafufufkan yanar gizo, sun canza yadda mutane ke mu’amala ta yau da kullun, dama yadda mutane ke magana, kai harma da yadda mutane ke soyayya a tsakanin juna.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG