Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lionel Messi Ya Rubuta Sakon ban Kwana Da Neymar


Lionel Messi da Neymar a lokacin karawar da FC Barcelona ta yi da Real Madrid a Camp Nou 3 Disamba, 2016.
Lionel Messi da Neymar a lokacin karawar da FC Barcelona ta yi da Real Madrid a Camp Nou 3 Disamba, 2016.

Rahotanni na cewa Neymar yayi ban kwana da abokan wasansa na FC Barcelona yana shirin komawa kungiyar PSG ta Faransa a kan zunzurutun kudi Fam miliyan 198.

LIonel Messi ya rubuta wani sako mai sosa zuciya na yin ban kwana da abokinsa Neymar, wanda ake kyautata zaton zai bar kulob dinsu ta FC Barcelona ya koma Paris Saint-Germnain, ko PSG, a kan kudin da ya wuce na kowane dan kwallo da aka taba saya a tarihi.

An ce a yau laraba, Neymar ya shafe kusan awa daya yana yin ban kwana da sauran abokan wasansa na Barcelona a wurin da suek samun horaswa, kuma nan ba da jimawa ba zai rattaba hannu kan takardar komawa PSG wadda zata saye shi a kan Fam miliyan 198, ko dala miliyan 256.

Yau laraba, Lionel Messi ya saka wani bidyo a shafinsa na Instagram, inda a ciki yake fadin cewa ya ji dadin shekaru da dama da suka yi suna buga tamaula tare da Neymar a Barcelona, kuma yana yi masa fatan alheri a inda zai koma.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG