Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zawarci Da Cinikayyar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A fagen saye da sayarwar 'yan wasan kwallon kafa na duniya, kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, ta cimman yarjejeniya kan cinikin dan wasan Monaco mai suna, Thomas Lemar akan kudi fam miliyan £45.

Everton ta sake taya dan wasan Swansea city, a karo na biyu, mai suna Sigurdsson a kan kudi fam miliyan £45.

Liverpool da Arsenal, sun nuna sha'awar su wajan sayen Karim Benzema, in har kungiyarsa ta Real Madrid, zata rabu dashi a bana.

Gareth Bale ya ce baya da sha'awar Komawa kungiyar Arsenal, domin maye gurbin Alexis Sanches.

Ita kuma Manchester United, ta ce tana da kwarin Guiwa wajen sayen Bale in har Real Madrid ta cimman nasarar sayen Kylian MBappe na Monaco.

Pep Guardiola na Manchester city, ya ce kungiyarsa ta na da karfin arzikin da zasu goga da Real Madrid, wajen sayen matashin dan wasan gabannan na Monaco Kylian MBappe.

Coutinho ya bukaci kungiyarsa ta Liverpool ta barshi ya Koma kungiyar Barcelona.

PSG ta debi wa'adin mako biyu don kammala cinikin dan wasan gaba na Barcelona Neymar inda ta saka zunzurutun kudi har fam miliyan £196 don ganin ta sayeshi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:11 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG