Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta saka zunzurutun kudi har fam miliyan £161 domin ta sayo matashin dan wasan gaba na Monaco, Kylian MBappe.

Westham ta kammala cinikin tsohon dan wasan Manchester united, wanda yake taka leda a kungiyar Bayern Leverkusen, mai suna Javier Hernandez,a kan kudi fam miliyan £16.

Da yuwar dan wasan Arsenal Alexis Sanches, zai amince da Komawarsa Manchester City, a maimakon PSG.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester, united Jose Mourinho, ya bada tabbacin bukatar Karin, 'yan wasa biyu kafin rufe hada hadar 'yan wasan bana.

Barcelona, ta tura wakilanta zuwa kasar Ingila kan batun sayen dan wasan Liverpool Philippe, Coutinho.

Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Monaco ta fara tattaunawa, da dan wasan gabanta Kylian MBappe don ya kara tsawaita kwantirakinsa a kungiyar, Real Madrid, da Manchester City, dai suna tsaye wajan ganin sun raba kungiyar Monaco da matashin dan wasan mai shekaru 18 a duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG