Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zinedine Zidane Bashi Da Tabbacin Zaman Gareth Bale A Kakar Wasannin Bana


Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, ta saw a kungiyar Barcelona kudi fam miliyan £133 in har tana son dan wasan gabanta Philippe Coutinho, mai shekaru 25.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa, ta Real Madrid Zinedine Zidane ya ce bai da tabbacin cewar dan wasan gabansa na gefe Gareth Bale, zai zauna a kungiyar a kakar wasan bana.

Shi kuwa mai horas da kungiyar Inter Milan Spalleti, cewa yayi kungiyarsa bazata sake Ivan Pericis a bana ba duk da Manchester united ta matsa lamba wajen zawarcin dan wasan.

Juventus, ta sake kunno kai a karo na biyu kan batun zawarcin dan wasan tsakiya na PSG Matudi, dan shekaru 30 a duniya.

Karim Benzema, ya ce yana tsammanin zai ajiye takalmam, taka ledarsa ne a Real Madrid, in lokacin sa yayi.

Paulo Dybala na kungiya Juventus, ya nuna sha'awarsa na ci gaba da zama a kungiyarsa, a kwanakin baya ne dai Barcelona, da Manchester united, suka nuna sha'awarsu wajan sayen dan wasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:11 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG