Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea da Manchester United Sun Cimma Yarjejeniyar Fam Miliyan 40


Nemanja Matic
Nemanja Matic

Kungiyoyin kwallon kafa ta Manchester United da Chelsea sun cimman yarjejeniya kan cinikin dan wasan tsakiya na Chelsea Nemanja Matic, dan shekaru 28 da haihuwa. Chelsea ta amince ta sayarwa Manchester United dan wasan akan kudi fam miliyan £40.

Mourinho wanda ya sayo dan wasan a lokacin yana mai horas da kungiyar Chelsea a shekara ta 2014 daga kungiyar Benfica, ya ce yayi kokarin dawo da dan wasan zuwa Old Trafford ne saboda har yanzu Matic yana da rawar da zai taka wajan taimakawa a Manchester United a kakar wasan bana,

A yanzu haka dai dan wasan na shirye shiryensa na zuwa duba lafiyarsa (Medical Check) domin fara fafatawa a kungiyar ta Manchester United.

Dubban magoya bayan kungiyar ta Manchester United ne suka nuna murnarso da sayen matic inda aka gansu reke da kyallayi mai dauke da hoton Nemanja sanye da rigar Manchester mai lamba 31 a filin atisaye,

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG