Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

David De Gea Na Iya Barin Manchester United Zuwa Real Madrid.


David De Gea
David De Gea

Manajan kulub din Manchester United Louis van Gaal, ya yarda da gaskiyar cewa mai tsaron gida David De Gea, na iya barin Manchester zuwa kulub din Real Madrid.

Ana dai kyautata zaton Real Madrid zatayi kokarin sayan mai tsaron gidan dan kasar Spain, a karshen rani.

Kwantaragin dan wasan dai zai kare a karshen kakar wasa mai zuwa da kulub dinsa Manchester United, amma har yanzu dai dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa bai saka hannu a wani sabon kwantaragin ba.

Louis van Gaal, manajan Manchester yace, “A duniyar kwallon kafa, komai na iya faruwa.” Alokacin da aka tambayeshi koyana da damuwa kasancewar Real Madrid na son sayan dan wasan. Yace, “muna son mu barshi a kulub din mu.”

David De Gea dai ya dawo Manchester a shekara ta 2011, daga kulub din Atletico Madrid inda aka sayeshi yuro miliyan 18 da dubu 900.

A farko farkon watan nan ne dai wakilin David wato Jorge Mendes, yace, “David dan wasan Manchester United ne kuma yana da kwantaragi dasu. Dole a mutunta hakan amma komai na iya canjawa cikin duk mintuna biyar.”

XS
SM
MD
LG