Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Ce Ko A Jikinta


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ce ba ta tsammanin za a garkama mata takunkumi irin na babbar abokiyar tsamarta, FC Barcelona, a bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, ta fara gudanar da bincike kan yadda Madrid ta sayi wasu ‘yan wasa matasan da shekarunsu bai kai 20 ba.

FIFA ta bukaci hukumar kwallon kafar kasar Spain da ta mika mata bayanai game da dukkan ‘yan wasa yara kanana dake wakiltar Madrid ko kuma kulob-kulob da suke hulda da ita.

A bara, FIFA ta haramtawa FC Barcelona sayen ‘yan wasa na wa’adi 2 na dibar sabbin ‘yan wasa a kan yadda ta keta doka wajen daukar ‘yan wasa yara daga 2009 zuwa 2013.

Madrid ba ta saba daukar sabbin ‘yan wasa a wa’adin dake farawa a watan Janairu ba, amma a bana, ta sayi Mink Martin Peeters da Martin Odegaard masu shekaru 16 kowannensu daga yankin Scandinavia, da Marco Asensio mai shekaru 19 dan Spain, da Lucas Silva dan Brazil.

FIFA ta ki yarda ta yi sharhi a kan wannan binciken da take gudanarwa.

XS
SM
MD
LG