Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tana Sama Tana Dabo A Equatorial Guinea


A yayin da ake kammala wasannin zagayen farko na gasar cin kofin kwallon kafar kasashen Afirka yau laraba a kasar Equatorial Guinea, kasashe 4 dake cikin rukuni na 4 ko D, zasu yi karon batta domin ganin ko za a iya fitar da gwani a tsakaninsu.

Dalili shi ne a tsakanin Kamaru da Cote D’Ivoire da Mali da Guinea, kowaccensu tana da maki bibbiyu, ta jefa kwallaye bibbiyu, an jefa mata kwallaye bibbiyu. Kowacce a cikin wadannan kasashe hudu, tana iya hayewa zuwa zagaye na biyu.

Jiya talata dai ba ta yi dadi ma kasar Senegal ba, wadda aka wayi gari tana ta deaya a rukuni na 3 ko C, amma a bayan wasannin jiya aka yi waje da ita baki daya, bayan da Aljeriya ta doke ta da ci biyu da babu ta haye saman wannan rukunin. Ita ma Ghana ta farfado daga ci daya da ATK ta fara jefa mata, ta rama, ta kuma kara guda aka tashi da ci biyu da daya, ta zamo ta biyu a wannan rukuni kuma zata haye zuwa wasannin kwata fainal.

A wasannin k,wata fainal da aka riga aka tsara kuma za a fara ranar asabar, Kwango Kinshasa zata kara da makwabciyarta Kwango Brazzaville yayin da Tunisiya zata hadu da mai masaukin baki Equatorial Guinea.

A ran lahadi, Ghana zata kara da wadda zata zo ta daya a bayan wasannin yau, yayin da Aljeriya zata jira wadda zata zo ta biyu a bayan wasannin na yau.

XS
SM
MD
LG