Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ivory Coast Ta Yi Gaba, Amma Mali Da Guinea Sai An Yi 'Yar Tinke


Kasar Ivory Coast ta haye zuwa ga wasannin kwata fainal na gasar cin kofin kasashen Afirka na kwallon kafa da ake gudanarwa a kasar Equatorial Guinea.

Ivory Coast ta vdoke kasar Kamaru da ci daya mai ban haushi a karawar karshe a zagayen rukuni-rukuni da aka buga yau.

A daya wasan na yau, an tashi kunnen doki a tsakanin Mali da Guinea, ma'ana, gobe alhamis za a yi 'yar tinke domin zaben wadda zata shige zuwa zagayen kwata fainal a tsakaninsu.

XS
SM
MD
LG