Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Christiano Ronaldo Zai Bar Kungiyar Real Madrid


Christiano Ronaldo

Shahararren dan wasan kwallon duniya Ronaldo zai bar kungiyar shi ta Real Madrid don zuwa kungiyar Juventus. Biyo bayan shekaru tara da ya kwashe a kungiyar ta Spain.

A jiya Talata kungiyar Madrid ta cimma matsaya da kungiyar Juventus bayan mika rokon Ronaldo da yayi na barin kungiyar, Juventures zata biya kungiyar Real Madrid dalar Amurka milliyan $123, don fansar dan wasan mai shekaru 33 da haihuwa.

Kungiyar ta nuna jin dadinta ga Ronaldo, don yadda ya nuna ma duniya cewar shi shahararren dan wasa ne na duniya, don kuwa ya kafa tarihi a kungiyar.

Yanzu haka Ronaldo yana hutu a kasar Greece, tun bayan cire kugiyar kwallon kafa ta Portual da akayi a gasar cin kofin duniya. Ronaldo dai a shekarar 2009 ya shiga kungiyar ta Real Madrid daga kungiyar Manchester United.

Ronaldo ya zura kwallaye 451 cikin wasanni 438, Ya taimakama kungiyar lashe wasanni 4, inda suka doke Juventures a shekarar 2017, kana ya taimakama kungiyar lashe wasannin laliga sau 2. Mun sami wannan labari ne daga shafin AP.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG