Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jack Wilshere Ya Gana Ido Da Ido Da Kocin Kungiyar Westham


A cigaba da hada hadar ‘yan wasan kwallon Kafa ta duniya da ake yi, Jack Wilshere sun Gana ido da ido da Kocin kungiyar Westham Manuel Pellegrini kan batun dawowarsa kungiyar bayan da dan wasan ya kammala dogon zamansa a kungiyar Arsenal a watan da ya gabata inda yanzu yake zaman kansa (free agent)

Arsenal zata rasa dan wasan Sevilla Ever, Banega dan shekaru 30 da haihuwa bayan da dan wasan ya yanke shawarar ci gaba da zama a kungiyar sa ta Sevilla.

Sabon Kocin Kungiyar Arsenal Unai Emery, ya ce zai sayar da wasu ‘yan wasan sa wajan ganin ya dauko dan wasan tsakiya na Barcelona Andre Gomes, mai shekaru 24 a duniya.

Everton ta tuntubi kungiyar Barcelona kan sayen dan wasan bayanta dan kasar Colombia Yerry Mina, mai shekaru 23, da haihuwa wanda ya fafata a gasar cin kofin duniya da ake yi yanzu 2018 a Rasha.

Mai tsaron raga na Westbromwich Ben Foster, mai shekaru 35, na shirin rattaba hannu a kungiyar Watford akan kudi fam miliyan £2.5.

Manchester city, ta kammala shirinta tsaf domin sayen dan wasan gefe na Leicester city, Riyad Mahrez, dan shekaru 27, da kuma dan wasan tsakiya na Napoli Jorginho bisa jimillar kudi fam miliyan 108.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG