Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwan Da Ke Gudana A Bangare Saye Da Musayar 'Yan Wasan Kwallo


Kungiyar Manchester city ta kammala shirinta tsaf domin sayen dan wasan gefe na Leicester city, Riyad Mahrez, mai shekaru 27, da haihuwa da kuma dan wasan tsakiya na Napoli Jorginho, bisa jimillar kudi fam miliyan £108.

Chelsea, tana bukatar zunzurutun kudi har fam miliyan 70 daga duk kungiyar da take bukatar sayen dan wasan tsakiyarta Willian, wanda Barcelona da Manchester United suka nuna sha'awarsu kan dan wasan inda a baya Chelsea, ta yi watsi kan tayin fam miliyan £50 da Barcelona tayi wa dan wasan dan kasar Brazil.

Liverpool ta motsa na ganin ta dauko dan wasan baya na Besiktas mai suna Domagoj Vida, wanda Everton take nema. Tottenham tana yunkurin dauko dan wasan tsakiya daga kungiyar PSG mai suna Adrien Rabiot dan shekaru 23 a duniya.

Sabon Kocin Arsenal Unai Emery ya bukaci dauko dan wasan tsakiya na kungiyar Barcelona Andre Gomes, sai dai ita kungiyar ta Barcelona tana bukatar karbar fam miliyan £30 kan dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG