Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe 8 Ne Za Su Kece Raini A Wasannin Kwata Final


A ranar Jumma'a 6 gawatan Yuli 2018 za'a cigaba da fafatawa a gasar cin kofin kwallon Kafa ta duniya wadda ke gudana a kasar Rasha 2018.

Kasashe takwas ne zasu kece raini amatakin wasan Kusa da na daf da na karshe (Quarter Final) inda kasar Uruguay, zata fafata da kasar Faransa da misalin karfe uku na rana agogon Najeriya, Nijar Kamaru da kasar Chadi,

Sai kuma wasan da zai fi daukar hankali tsakanin Brazil, da kasar Belgium, a haduwarsu da suka yi a shekarun baya, Brazil ta samu nasara akan Belgium, a gasar cin kofin duniya na 2002 da ci 2-0 a matakin zagaye na sha shida wanda ‘yan wasan Brazil Rivaldo, da Ronaldo, suka jefa mata.

Sai kuma ranar Asabar 7/7/2018 za a kara tsakanin kasar Sweden, da England, su kuma masu masaukin baki kasar Russia, zasu gwabza ne da Croatia.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG