Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kocin Kwallon Kafar Masar Hector Cuper Yayi Murabus


Maihoras da tawagar 'yanwasan kungiyar kwallon Kafa ta kasar Masar maisuna Hector Cuper. ya bar mukaminsa a matsayin kocin Masar, bayan da aka fitar da su daga gasar cin kofin duniya na bana wanda yake gudana a kasar Rasha.

Kocin mai shekaru 62 da haihuwa dan kasar Argentina, wanda yarjejeniyar shi da kwantirakinsa zai kare a bayan kammala gasar cin kofin duniya na 2018, sai dai bayan dawowarsu daga kasar Rasha, sunyi wata ganawa da hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Masar (EFA).

Inda dukkaninsu suka yanke shawarar yi masa godiya dashi da abokan aikinsa, musamman nasarar da ya jagoranci kungiyar ta kai zuwa ga wasan cin kofin kwallon Kafa na nahiyar Afrika, bayan shekara uku rabonsu da kaiwa.

Hakan kuma ya taimaka wa kasar ta samu zuwa gasar cin kofin duniya wanda ta shafe shekaru 28 bata jeba. Kocin ya fara aiki a matsayin sa na maihoras da kasar Masar, tun shekara 2015, Kasar Masar dai ta fice daga gasar ta bana ba tare da maki ko daya ba, inda a wasanta na farko kasar Uruguay aka doketa 1-0 wasa na biyu Russia 3-1 sai kuma Saudi Arabia, ta Shata 2-1.

Wasu na alakanta hakan saboda rashin lafiyar Fitaccen danwasansu, Mohammad Salah inda bai samu damar buga wasan farko ba a gasar cin kofin duniya. Sai dai ya jefa kwallaye biyu a wasanni biyu da ya buga na karshe.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG