Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Borussia Dortmund Ta Sa Wa Alvaro Morata Fam Miliyan 45


A bangaren hada hadar ‘yan wasan kwallon Kafa ta duniya wadda ake cigaba da yi na watan yuni, Kungiyar kwallon Kafa ta Borussia Dortmund tana zawarcin dan wasan gaba na Chelsea Alvaro Morata, inda ta sanya masa kudi fam miliyan 45 a tayin farko.

Dan wasan baya na kasar Spain Mai taka leda a kungiyar kwallon Kafa ta Barcelona Jordi Alba, mai shekaru 29, da haihuwa ya bukaci ya cigaba da zama a kungiyarsa ta Barcelona, maimakon ya koma Kungiyar Tottenham kamar yadda ta nuna sha'awarta akan sayen dan wasan.

Har Ila yau Kungiyar Tottenham, ta nuna sha'awarta kan dan wasan kasar Croatia Ante Rebic, dan wasan da yanzu haka yake haskakawa a gasar cin kofin kwallon Kafa ta duniya da yake gudana a kasar Rasha, Kuma yana taka ledarsa ne a kungiyarsa ta Eintracht Frankfurt.

Juventus ta bayyana ra'ayinta na dauko dan wasan tsakiya na CSKA Moscow mai suna Aleksandr Golovin, dan shekaru 22, a duniya wanda kungiyar Arsenal, Chelsea, da Barcelona, suma suke zawarcinsa.

Manchester united ta kammala cinikin dan wasan tsakiya na Shakhtar Donetsk mai suna Fred dan kasar Brazil akan kudi fam miliyan £52.5 bisa yarjejeniyan kwantirakin shekaru biyar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG