Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Saye Da Sayar Da Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Kungiyar kwallon Kafa ta Manchester United na bukatar rike mai tsaron ragar ta David de Gea har zuwa lokacin da zai ajiye takalman taka leda. Dan wasan wanda yanzu ya rage masa saura watanni 18 ya karkare kwantiragi a kungiyar 2020.

Yanzu haka dai Mataimakin shugaban kungiyar Ed Woodward, na shirin tattaunawa da dan wasan inda suke yunkurin bashi kudi fam dubu £250 duk sati mai makon £190.

Arsenal tana tattaunawa kan batun dauko dan wasan gaba dan kasar Gabon mai taka Leda a kungiyar kwallon Kafa ta Borussia Dortmund, Emerick Aubameyang, domin ya maye mata gurbin Alexsi Sanchez wanda yake shirin barin Kulob din a watan Janairu nan.

Arsenal ta sa fam miliyan £53 tayin farko akan Aubameyang, Everton tana kokarin kammala cinikin dan wasan gefe na Arsenal Theo Walcott 28 akan kudi fam miliyan £20 a wannan satin.

Kungiyar kwallon Kafa ta Liverpool ta jera sahu cikin tawagar kungiyoyin Manchester united da Manchester city wajan zawarcin dan wasan gaba na Arsenal Alexsi Sanchez 29.

Ita kuwa Arsenal tana zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester united Henrick Mkhitaryan ne inda ta ce tana bukatar cinikin dan wasan ya kasance cikin sayen Sanchez da Manchester united ke son yi.

Ita kuwa Manchester united tana shirin maida Sanchez dan wasa mafi tsada a Firimiya lig na kasar Ingila in har ya amince da ya tafi Kungiya inda zata bashi fam dubu £350 a sati a matsayin albashi.

Chelsea tace har yanzu tana kan batunta na dauko dan wasan gaba na Westham Andy Carroll 29 a matsayin aro. Liverpool ta ce ta janye daga batun zawarcin dan wasan gefe na Monaco Thomas Lemar bayan da kungiyarsa ta bukaci fam miliyan £90 ga duk mai bukatar dan wasan 22.

AC Milan ta ce ba zata sayarda da dan wasan tsakiya mai suna Suso da za'a biya fam miliyan £80, Kungiyar kwallon Kafa ta Saint-Etienne ta kasar faransa tana tattaunawa dan ganin ta dauko dan wasan baya na kungiyar Arsenal. Mathieu Debuchy. 32

Arsenal da Chelsea sun jera sahu daya wajan zawarcin dan wasan gaba na kungiyar Watford mai suna Richarlison, Tuni dai Kocin Arsenal Wenger da Antonio Conte ko wannensu ya gana da wakilin dan wasan kan batun.

Westbromwich ta saka fam miliyan £12 wajan sayen dan wasan tsakiya na Fulham kuma Karfin mai suna Tom Cairney inda take yunkurin karawa zuwa fam miliyan £15 ddomin ganin ta dauko shi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG