Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Gawurtaccen Barawon Shanu a Birnin Kebbi


‘Yan sanda a jihar Zamfara sun kama wani gawurtaccen barawon shanu mai suna Adamu Bello, wanda kuma ake yi wa lakabi da Adede.

Bayan kasancewa barawon da ya kware wajen satar shanu an kuma ce Adede na fashi da makamia a ciki da kewayen karamar hukumar Bagudo da ke jihar Kebbi.

Kamen Adede tare da wasu su hudu da ake tuhuma da laifin sata, fashi da makami zuwa shelkwatar ‘yan sandan Birnin Kebbi, na cikin gagaruman nasarorin da aka samu tun bayan fara aikinsa a cewar kwamishinan ‘yan sanda Yakubu Jibrin.

Ya kuma ce, an taba tuhumar Adede a baya da laifin satar shanu a wata kotu garin Bussa na jihar Neja, amma bai yi ladama ba sai ma ya kara kaimi wajen aikata ayyukan assha.

Kwamishinan ya kara da cewa shi da abokan aikinsa (‘yan sanda) na jihar Kebbi, sun yanke shawarar kawas da ayyukan ta’assa a jihar a karshen shekarar nan ta 2015 har zuwa nan gaba.

XS
SM
MD
LG