Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ba Tsaffin 'Yan Bautar Kasa 173 Tukuici


A yau laraba gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba wasu matasa 173 da suka kammala bautar kasa NYSC a shekarar 2012, da 2013, da kuma 2014 tukuicin takardar daukar a bangarori daban daban dake karkashin ma’aikatar gwamnatin tarayya.

Hukumar kula da ma’aikata ta gwamnatin tarayya ce ta mika ma matasan tukuicin takardar daukar aiki, kuma hukumar ta bayyan cewa matasan guda 173 sun yi fice wanda ya babnbanta su daga sauran matasa a yayin da suke ayyukan yi ma kasa hidima.

A yayin da ake mika masu takardar daukar aikin, shugaban hukumar Mr Deaconess Joan Ayo ya bayyana cewa an ba matasan wannan kyautar ne a sakamakon irin ficen da suka nuna a cikin shekarun da suka gudanar da ayyukan bautar kasar.

Shugaban yace “ina taya ku murnar samun wannan nasarar, kun yi kokari kwarai da gaske, kuma hakan ya nuna cewa kuna cikin daliban da suka yi aiki tukuru tun daga jami’a, shi yasa a lokacin bautar kasar ma kuka banbanta kawunan ku da sauran matasa.

Ya kara da cewa, anyi la’akari da can cantar da matasan suka yi shi yasa aka dauke su aiki, kuma hakan baida wata nasaba da siyasa ko tantancewar hukumar tantance ma’aikata”.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG