Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uba Da ‘Dansa Sun Saci Fuka Fukan Kaji


An kama Uba da ‘Dansa bayan da suka saci fuka fukin kaji har na kudi kimanin dalar Amurka dubu 41, kwatankwacin Naira miliyan takwas da dubu ‘dari biyu, wanda suka sata daga wani gidan abinci a birnin New York kuma saka sayar wa wasu gidajen abinci a yankin.

Jami’an tsaro dai sunce mutumin mai suna Paul Rojek shekaru 56 shi da ‘dansa Joshua Rojek mai shekaru 33 da haihuwa, an kamasu ne alokacin da suke satar ne a gidan abincin da ake kira Twin Trees Restaurant da ke garin Syracuse a Amurka.

Baki ‘daya mutanen biyu na aiki ne a matsayin masu girki a gidan abincin, kuma suna yin odar fuka fukan kajin ne da sunan gidan abincin da suke ma aiki, jami’an sunce bayan an kawo odar sai mahaifin da ‘dansa su kwashe kayan domin zuwa su sayar cikin karyayyen farashi a wasu gidajen abinci na dabam.

Manajan gidan abincin dai ya fara zargi bayan da ya ankara sun biya kudi kimanin dalar Amurka dubu 41 tsakanin watan Fabarairu zuwa 21 ga watan Nuwamba. Ana tuhumar mutanen biyu da laifin sata da yin amfani da kudin kamfani don bukatar kansu. Babu tabbacin ko suna da lauyan da zai kare su a hannu, kuma wanda zai yi bayan kan abinda ya faru.

XS
SM
MD
LG