Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kanye West Da Kim Kardashian Sun Sanya Ma Dansu Suna Saint West


Tauraron mawakin nan na Amurka Kanye West da matarsa Kim Kardashian sun sami karuwa ranar Asabar din da ta gabata.

Biyo bayan matsalar daukar juna biyu da Kim ta fuskanta, tauraruwar wasan talabiijn din da ake kira “Keeping up with the Kardashians” da Mawakin Mijinta sun sami da namiji bayan diya mace da suke da ita, kuma Kim ta sanar da labarin a kafar sada zumunci.

Jiya litinin kuma Kim ta bayyana nauyin yaron wanda ya kai kilo 3.8 a lokacin da aka haife shi.

Tun bayan samun labarin haihuwar yaron, jama’a da yawa sun yi ta tunani da hasashen sunan da iyayen za su ba shi. Amma Kim Kardashian ta Sauwake masu duk wani hasashen da tunani a lokacin da ta sanar ta kafar Twitter cewa sunan dansu "Saint West".

XS
SM
MD
LG