Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Harsashen Maye Gurbin Zanedine Zidane A Real Madrid


Zinedine Zidane
Zinedine Zidane

Yayinda da kungiyoyin kwallon kafa suke shirye shirye domin sayen ‘yan wasa a watan Janairu dubu biyu da goma sha takwas lokacin da za a bude saye da sayarwa na ‘yan wasan.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florentine Perez da mai horar da kungiyar Zinedine Zidane sunce sun samu tattaunawa da dan wasan kungiyar kwallon kafa na Chelsea Eden Harzard kan batun dawowarsa kungiyar ta Real domin ya tallafa wa Cristiano Ronaldo.

Haka kuma kungiyar tace tana iya yuwar zata sallami Antonio Conte domin ya maye gurbin Zinedine Zidane a matsayin mai horar da kungiyar ta Real Madrid.

Westham da Everton na zawarcin mai tsaron baya na kungiyar Westbromwich mai suna Jonny Evans mai shekaru 29, da haihuwa.

Kungiyar Manchester United tace zata ba da Juan Mata da Karin kudade wa kungiyar Inter Milan kan batun sayen Joao Mario daga kungiyar ta Inter.

Southampton, Newcastle da Crystal palace suna zawarcin mai tsaron baya na kungiyar Dundee, mai suna Jack Hendry a watan Janairu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG