Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanya Mafi Saukin Isar Da Sako Ga Al'umma - Inji Shafiu Muhammad


Shafiu Muhammad
Shafiu Muhammad

Ina da tabbacin cewar waka ita ce hanya mafi sauki da za’a iya canza al’umma ba tare da an kai ruwa rana ba su fahimci sakon da ake so a isar musu cikin raha da ilmantarwa inji mawaki ‘Shafiu Muhammad, wanda aka fi sani da Baba-G.

Baba-G dai mawakin fina-finan Hausa da kuma hip hop ne wanda ya ce ya zabi hip-hop ne saboda isar da sakonni cikin hanya mafi sauki mai kuma nishadantarwa.

Har ila yau, matashin yana wakokin fina-finai, ya kuma kara da babban burinsa dai al’umma ta amfani da wakokinsa, sannan ya kara da cewa babban kalubalen da yake fuskanta shine yadda wata rana idan ya tashi da niyyar waka kuma akayi rashin sa’a yana wani yanayi na rashin jin dadi sai wakar ta ki yiwuwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:04 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG