Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cinikayya Tsakanin Kungiyoyin Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


José Mourinho
José Mourinho

Mai horas da kungiyar Manchester united Jose Mourinho, ya ce zai kashe kudi fam miliyan £80m a cikin watan Janairu domin sayen wasu ‘yan wasa amma da yuwuwar za'a samu wadannan kudaden ne ta hanyar sayar da Luka Shaw, da kuma Matteo Darmian.

Mai tsaron raga na kungiyar Chelsea Thibaut Courtois, mai shekaru 25, zai iya yin watsi da sabuwar kwantaragi a kungiyar Chelsea, koda kuwa kulob din zai kara masa albashi irin na David De Gea, ba Manchester United.

Madrid ta nuna shi'awar ganin ta sayo dan wasan na Chelsea, Eden Hazard, don ya taimaka wa Cristiano Ronaldo, a kungiyar.

Arsenal ta ce ta shirya sayar da dan wasanta Theo Walcott, a watan Janairu a tsakanin tsohon Kulob din sa Southampton ko kuma Westham.

Real Madrid, ta na zawarcin Kaftin din kungiyar kwallon kafa na Inter Milan Mauro Icardi, à watan Janairu mai zuwa.

Manchester united, ta ce tana da karfin gwiwa wajan sayen dan wasan baya na Tottenham, Danny Rose, akan kudi fam miliyan £50, A watan Janairu ko kuma karshen kakaR wasan bana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:37 0:00

Leonal Messi, ya bukaci Barcelona, ta jinginE batun sayen dan wasan tsakiya na Liverpool, Philippe Coutinho, ta maida hankalin wajan neman mai tsaron baya a kungiyar.

Mai horas da kungiyar Manchester city, Pep Guardiola ya ce ya dawo da karfin gwiwa kan sayen Alexsi Sanches, daga Arsenal, a watan Janairu mai zuwa.

Shi kuwa mai horas da kungiyar Inter Milan, ya ja hankalin dan wasanne wanda Manchester united, take zawarci tun a farkon kakar wasan da ya cigaba da zama a kungiyar maimakon ya Koma Manchester,

Southampton, Newcastle da Crystal palace sun jera sahu wajan sayen mai tsaron baya na kungiyar Dundee, mai suna Jack Hendry a watan Janairu.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG