Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasan Carling Cup 2016/2017 (Quarter Final)


A jiya Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tayi waje da Kungiyar Leeds United a

gasar English Football League, ta 2016, da ci 2 da 1. Itama Hull City ta samu nasarar doke kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United da ci 3 da 1 bayan an shafe mintuna casa'in inda akayi 1-1 daga bisani aka kara mintuna talatin kafinnan Hull city, suka samu nasara.

Wannan nasara ta ba da dama ga Liverpool da Hull City, zuwa zagayen kusa da na karshe wato Semi final inda suke jiran kungiyoyin da zasu fafata a yau inda kungiyar kwallon kafa ta Arsenal zata kara da Southampton, ita kuwa Manchester United, zata karbi bakuncin Westham, ne a Old Trafford, da misalin karfe tara na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da Chadi.

A can kasar Spain ma haka abin ya wakana a gasar cin kofin Copa del Rey, 2016/2017.

Leganes 1-3 Valencia

Sporting Gijon ta sha kashi a hannun Eibar da kwallaye 2-1

Alcarcon tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Espanyol

Real Betis ta doke Deportivo daci 1-0

A yau kuma za'a kara tsakanin Toledo da Villarreal

Real Madrid da Cultural Leonesa

SD Formentera zasu karbi bakuncin Atletico Madrid

Guijuelo da Celta vigo

Cordoba da Malaga

Granada zasu kece raini da Osasuna

Yayinda Hercules zasu fafata da Barcelona

Za'ayi wasanne a lokuta daban daban agogon Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG