Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Diego Costa
Diego Costa

A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta ware zunzurutun kudi har fam miliyan £50 domin sayen dan wasan gaba na Chelsea mai suna Diego Costa.

Arsenal na neman dan wasan kasar Ukraine mai suna Oleksandr Zinchenko, inda, ita PSG ita kuwa na zawarcin Faouzi Ghoulam daga Kungiyar kwallon kafa ta Napoli.

Har ila yau Inter Milan na yunkurin sayen dan wasan gaba na Arsenal Alexis Sanchez.

Shi kuwa Toni Kroos na Real Madrid ya ce yana ganin ya kamata ya ajeyi takalmansa na taka leda da zaran kwantareginsa ya kare domin a lokacin zai cika shekaru talatin da biyu da haihuwa a duniya inda zai fuskanci wasu abubuwa daban.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:58 0:00

XS
SM
MD
LG