Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dad'i Na Da Gobe Saurin Zuwa! Gobe Dan-Wasa Tiger Zai Bayyana!


Dan Wasan Kwallon Golf Tiger Woods!
Dan Wasan Kwallon Golf Tiger Woods!

A gobe ne idan Allah, ya kaimu ake sa ran dan wasan kwallon rami “Golf” Tiger Wood, zai koma fagen daga, biyo bayan kwashe tsawon fiye da watannin goma sha biyar 15, da yayi a bayan fili.

Ana dai sa ran dan wasan zai dawo da karfin shi, sanadiyyar kwashe lokaci mai tsawo yana jinya. Tiger, dai shine shahararren dan wasan kwallon rami a fadin duniya, biyo bayan lashe wasannin biyar 5, da yayi da suka kai shi a matsayin da yake.

Ya bayyanar da cewar, lallai a shirye yake, kuma yana matukar murna da zagayowar wannan wasan. Ana sa tsanmanin cewar, dan wasan zai shiga cikin jerin sunayen zakaru hamsin 50, na duniya.

Cikin jawabin shi lokacin da yake bayani jiya, yace “idan mutun bai tashi tsaye ba, to taya Allah, zai taimake shi a kan duk wasu burin shi na rayuwa?” Sai ya kara da cewar, “Duk wanda yake neman zama wani abu a duniya, to babu shakka sai ya tashi haikan wajen nema kamun ya kaiga nasara, rashin lafiyar shi ba wata abu bace illa jarabawa”

Ya tabbatar ma masoyan shi cewar, zai kokarta ya cigaba da abun da ya saba yi a baya. Kana ina bukatar ku tayani da addua, inji Tiger Wood.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG