Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wikk Tourist Ta Lallasa Gombe United A Gasar North East Free Season 2016


Wikki Tourist
Wikki Tourist

A shirye shiryen da manya manyan Kungiyoyin kwallon kafa na Najeriya keyi na fuskantar gasar firimiya lig ta bana, a yanzu haka kungiyoyin sun dukufa wajan zakulo haziqan 'yan wasa daga sassa daban daban domin shiri a gasar ta bana.

Bayan haka kuma Kungiyoyin sukan hada wasanni mai taken (Free Season) a can yankin arewa maso gabas, kuma ana hada irin wannan wasa ne inda kungiyoyi guda hudu da suka fito daga yankin suke fafatawa a tsakaninsu acan jihar Gombe

Kungiyoyin sune Wikki tourist dake garin Bauchi, Gombe United, sai El-kanemi ta jihar Maiduguri, da kuma Kungiyar kwallon kafa ta Doma, dake jihar Gombe.

A karawar da sukayi a tsakaninsu Wikk tourist ta doke Gombe United, da ci1-0 sai El-kanemi sukayi kunnen doki 1-1 da Doma, a karawar da Gombe United, ta yi da El-kanemi. Gombe United ta samu nasara daci 2-0 hakanan Doma, ta sake yin kunnen doki 1-1 tsakaninta da Wikki, In da yau ake tsammanin za'a buga wasa tsakanin Gombe United da Doma

Wikk tourist da El-kanemi ta Maiduguri, sai dai haka bai yuwuba saboda wasu dalilai wanda ba'a baiyana suba.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG