Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Kwallon Rami "Tiger Woods" Ya Sanar Da Dawowar Shi Da Karfi!


Dan wasan kwallon rami Tiger Woods
Dan wasan kwallon rami Tiger Woods

A jiya Talata ne shahararren dan wasan kwallon rami “Golf” Tiger Woods, ya bayyanar da cewar, ya shirya dawowa fagen wasa. Yana sa rana a farkon watan Disamba, zai fara karyawa da wasa, bayan kwashe tsawon lokaci yana jinya.

Tun dai a watan Augusta na shekarar da ta gabata, dan wasan bai sake buga wasaba, yan zu haka dai ya shirya buga wasa daga ranar 1 zuwa 4 na watan Disamba. Inda yake kalubalantar abokin karawar shi, wanda shima zakaran gwajin dafi ne a fagen wasan golf. A gasar wasan zakaru na cin kofin Albany, a filin wasan dake Bahamas.

Dan wasan Tiger, ya bayyanar da cewar “Ina mai matukar farincikin dawowa ta fagen wasa. Domin kuwa rabona da buga wannan wasan gasar, tun a shekarar 2014" Idan dai ba’a manta ba, a ‘yan kwanaki da suka gabata ne ya kamata dan wasan ya buga wasan kamfani Safeway, wanda a ‘yan kwanaki kadan da wasan ya fitar da sanarwar ba zai samu damar buga wasan ba.

Ya kara da cewar, bayan shi da ya bashi matsala, a lokacin baya, yanzu ya warke don haka yanzu dai-dai yake da kowa a fagen wasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG