Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hada Hadar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


A hada hadar 'yan wasan kwallon kafa na duniya, shahararan dan wasa kwallon kafa na kasar Wales mai taka leda a kungiyar Real Madrid Gareth Bale ya sake rattaba hannu wa Kungiyar sa ta Real Madrid na tsawon shekaru shida inda zai kare a 2022.
Bale ya taho kungiyar Real Madrid, ne a shekara ta 2013 daga Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham akan kudi fam miliyan £85 a wanann lokacin shine dan wasan da yafi kowa tsada.
Gareth Bale ya fafata wasanni wa Real Madrid har sau 130 ya jefa kwallaye guda 62 a raga .
Manchester United na zawarcin dan wasan baya na Real Madrid mai suna Pepe dan shekara talatin da ukku da haihuwa.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na neman dan wasan Celtic mai suna Moussa Dembele akan kudi fam miliyan £40m Kungiyar Real Madrid da Manchester United da kuma Manchester City na zawarcin dan wasan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG