Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu Ya Sha Gaban Cristiano Ronaldo


Dan kwallon kungiyar Real Madrid, Gareth Bale, yanzu zai kwashe kudade har Fam 350,000, duk mako, a kungiyar ta Real Madrid.

Wannan ya biyo bayan amincewar da yayi na kwantaregin Karin shekaru shida a kungiyar ta Real Madrid.

A wannan makon ne aka zabi dan wasa Gareth Bale, ya kasance cikin wadanda zasu yi takarar neman cin kambin Ballon d’Or, na bana, shi dai wannan dan wasa a shekarar 2013, ne ya zo kungiyar Real Madrid, daga kungiyar Tottenham.

Shima Cristiano Ronaldo, wanda ke kwasan Fam 288,000, kowane mako an fara sabon tattaunawa dashi akan wani sabon kwantaregi, ana kuma sa ran cewa zuwa kashen shekara zai kasance cewa albashin sa zai fi na kowa a kungiyar ta Real Madrid.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00

XS
SM
MD
LG