Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Mata 7 Daga Wurare Daban Daban Da Hoton Saurayi Guda A Shafin Sada Zumunta


Litini uku ga watan Oktoba, ta kasance ranar da ‘yan mata ke tunawa da samari masoyansu inda akasari kan Makala hoton saurayin da suke kauna akan shafin sada zumunta na yanar gizo musamman facebook ko twitter domin kawaye su kalla kuma su tofa albarkacin bakin su.

A wannan rana ce dai wasu ‘yan mata guda bakwai daga wurare daban daban suka Makala hoton wani saurayi guda a matsayin saurayin su.

Lamarin ya faru ne yayin da masu sa ido akan shafukan sada zumunta na twitter suka lura da cewar wasu ‘yan mata daga wurare daban daban sun Makala hoton saurayi guda, kuma sanye da kaya iri guda, kuma dukkan su ke ikirarin matashin a matsayin saurayin da kowace ke kauna.

Abin tambaya a nan shine, yaya aka yi wadannan ‘yan mata guda bakwai daga wurare daban daban masu nisa suka sami hoton saurayi guda kuma duka suka Makala shi a shafin sada zumunta na twitter a matsayin wanda suke kauna a zuciyar su.

Kuma shi saurayin, ta yaya ya sami wadan nan ‘yan mata daga bangarori daban daban har suke kaunarsa ta yadda lamarin ya kaiga Makala hoton sa a matsayin wanda kowacce a cikin su ke kauna?

Idan kai ne, ko kece wannan lamari ya shafa me zaki yi ko me zaka yi?

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG