Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Sayarda 'Yarta Naira 50.000


Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, ta cafke wata mata mai suna Grace Onome, wace ake zargi da sayarda ‘yarta mai shekaru biyu da haihuwa.

Ita dai wannan mata ta sayarda ‘yar tata ne akan kudi Naira dubu hamsin, an kuma cafke tane a yankin Badagry da wasu mutane hudu wadanda suka taimaka wajan sayarda yarinyar.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar, SP Dolapo Badmos, wanda ya tabbatar da labarin, yace ita dai Onome wace it ace mahaifiyar Zainab, yarinyar da aka sayarda aikin karuwanci take yi kuma karuwa ‘yar uwarta ta sayardawa mai suna Endurance.

Ita wace ta saye yarinyar tayi gaba da yarinyar amma kakakin ‘yan Sandan yace suna bin sahun ta domin tabbatar da ganin cewa sun gano ta tare da yarinyar.

XS
SM
MD
LG