Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsayin MOPPAN Dangane Da Jaruma Rahama Sadau


A yayin da ake ci gaba da kace nace dangane da korar Rahma Sadau daga masana’antar kannywood, Shugabannin Hadaddiyar kungiyar masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, wato MOPPAN, ya ce rungumar da Rahama Sadau ta yi wa Classiq, ta sanya mutane suna yi musu kallon mutanen banza.

Ya kara da cewa sau uku ke nan Rahama na aikata irin wannan danyen aiki, a inda a wannan karon har sai da aka yi kuri'a kuma masu son a kore ta suka yi rinjaye.

Akan haka ne muka zanta da jamian hulda da jama’a na haddadiyar kungiyar Mopan reshen jihar kano Balarabe Murtala Baharu dangane da wannan batu

Ko da yake a yunkurin mu na jin ta bakin jaruma Rahma Sadau ya ci tura.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:46 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG