Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Bude Makarantun Kwana A Jihar Borno


Gwamnatin jihar Borno, ta ce ranar litinin 10, ga watan Oktoba, zata bude duk makarantun kwana na jihar, da suka kasance a rufe fiye da shekaru biyu Kenan, sakamakon sace dalibai mata na makarantar garin Chibok.

Gwamnatin ta ce za’a dai bude wadannan makarantun ne a inda aka ga cewa suna da tsaro, inda kuma aka ga cewa akwai ‘yan matsaloli za’a kaisu wadansu garuruwan ne domin su ci gaba da gudanar da karatun su.

Kwamishinan ilimi na jihar ta Borno, Musa Inuwa Kubo, ya shedawa muryar Amurka cewa yanzu haka Gwamnatin jihar Borno, ta kammala dukkan shirye shiryen ta na sake bude irin wadannan makarantun kwana, wanda ya ce a yanzu haka akwai wasu makarantun sakandare amma na jeka ka dawo wadanda suke gudanar da karatun su.

Ya kara da cewa a wannan karon za’a bude makarantun kwanan ne wadanda suka hada da na mata da maza da yace adadin su ya kai saba’in da biyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

XS
SM
MD
LG