Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malamar Dalibai Nakasassu Ta Karramasu A Ranar Auren Ta!


Malama Da Dalibai A Wajen Auren ta
Malama Da Dalibai A Wajen Auren ta

Aikin koyarwa, ba wai kawai ta tsaya a makarana bane ko a aji, tsakanin malamai da daliban su. Wata malamar firamari, ta dauki dangantakar ta da dalibanta zuwa mataki nagaba. Kinsey French, malamace da take koyar da yara masu nakasa, ko bukatar taimakon gaggawa.

A dai-dai lokacin da take shirye-shiryen bukin ta, ta bayyana ma mijinta cewar lallai wannan bukin nasu, ba zai kayatuba idan wasu mutane basu halarci bukin ba, tanaganin cewar lallai idan wadannan mutane basu zo ba, ta babu shakka za’a iya fasa bukin.

Kowa daga dangin ta zuwa dangin mijin, sunyi mamakin suwanene wadannan mutane, da suke da matukar muhimanci a rayuwar ta, da suka wuce sabon angonta? Ranar buki bayan kowa ya hallara, sai tace sai an jira manyan baki.

Jim kadan sai ga manya-manyan baki sun iso, koda aka bude mota sai ga kananan yara sun fito daga cikin motar, nan da nan sai ta gabatar da yaran a matsayin manyan baki, da suke faranta mata rayuwa, kuma sune dalibanta da take koyarwa.

Mintoci kadan daga isan dalibanta, sai ta umurci malamin da ke daura aure da ya cigaba da daurin aure, tunda rabin rayuwar ta sun iso, hakan na nuni da cewar babu wani malami da yaci tutar zama malami, batare da yana da kyakyawar dangantaka tsakanin shi ko ita da daliban suba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG