Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wayoyin Hannu Na Yada Cututtuka Cikin Sauki!


Wayar Hannu
Wayar Hannu

Domin gujema cututtuka da ake dauka tsakanin mutane, wasu taron masana sun bayyanar da wasu hanyoyi guda shida da suka tabbatar da cewar, sune hanyoyin yada cututtuka a tsakanin jama’a, batare da mutane sun bada hankalin su wajen ba.

Maganin wadannan cututtukan guda uku ne, mutun ya kokarta yin allurar riga kafi, a wannan yanayin, haka a guji zama da mutane dake da mura, tari ko wata cuta da wani kan iya dauka, sai a hanzarta don tsaftace muhalli da wanke ko gyara waje bayan tashin mara lafiya.

Wayoyin hannu na daya daga cikin hanyoyin da ake daukar cuta cikin sauri da sauki, yadda mutane ke rike waya a hannu bayan cuttuka sun gama zagaye wayar. Haka da yadda mutane ke shiga wajen jama’a batare da saka wani kariya ba, koda kuwa wajen bude kofa ne, don wani yana dauke da wata cuta kuma ya sakata a jikin hannu kofa.

Haka ma mutane suyi hattara da yadda suke amfani da irin kayan da akanyi aron su, kamar kaset, rumot control, da dai makamantan su. Da kiyaye wadannan abubuwa ne kawai mutun zai iya gujema cututtuka dake yaduwa a tsakanin mutane.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG