Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hauwa Liman: Bunkasar Tattalin Arzikin Kasa Nada Alaka Da Ilimin 'Ya-Mace!


Hauwa Liman
Hauwa Liman

Hauwa Liman, matashiya ce da take kokarin ganin matasan Arewacin Najriya, sun farga, sun fuskanci alkiblar cigaba. 'Yar asalin garin Daura ce a cikin Jihar Katsina. Tayi karatun firamare a Model Staff School, F.G.C Daura. Daga nan ta tafi Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta ‘Yanmata da ke garin Bakori a Jihar Katsina, inda ta yi karatun sakandare. Daga nan ta sami shiga Jami’ar Bayero da ke garin Kano inda ta karanci Tattali (Economics).

Ta yi bautar kasa a jihar Enugu a shekarar 2009. Daga nan ta sake komawa Jami’ar Bayero ta samu digiri na biyu a kan Cigaban Al’umma (Development Studies). Ta samu halartar kwasakwasai da dama da tarurrukan kara wa juna sani musamman a kan hada-hadar kasuwanci da harkokin mata da matasa.

Hauwa itace shugaban kamfanin AFRIK ABAYA kamfani ne da yake samar da sutura ta mutunci ga mata, musamman mata ma’aikata da daliban sakandare da na Jami’a. Bugu da kari, Hauwa ta kirkiri FASHION FOR DEVELOPMENT INITIATIVE (FODI), wanda shiri ne da ke wayar wa da mata kai, musamman ‘yan sakandare akan muhimmancin ilimin ‘ya mace, sannan ya kuma basu damar koyon sana'o'in hannu domin dogaro da kai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG