Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salisu Abdullahi: Shugaban Kamfanin Bola Zuwa Aljihu!


Salisu Abdullahi
Salisu Abdullahi

Muhammad Salisu Abdullahi, matashi dan shekara 25 ne, kuma haifaffen garin Azare, a karamar hukumar Katagum, Bauchi, Nijeriya. Salisu shine makirkirin kuma shugaban kamfanin Haleematus-Sa`adiyya Enterprises. kamfanin da yake sarrafa ledodin pure water da sauran kayan roba a jihar Bauchi.

Salisu har ila yau shine shugaban zangon matasan da suka dauki aniyar kirkiro da sabon kamfani na zamani na gudanar da saraffa shara (waste management), wanda ake kira, “AREWA eTrash2Cash” a jiha mafi girma a arewa, wato birnin Kano. Salisu yayi karatun Firamary da na Sakandire a Islamic Orientation Primary and Secondary School, daga shekarar 1997 zuwa 2009, dake garin na Azare, a jihar Bauchi. A shekarar 2010, ya tafi jami`ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda ya karanta fannin kimiyya ta lafiya, wato, BSc Biochemistry, ya kuma kammala karatun a shekarar 2015. A wannan shekaran ya tafi bautar kasa na shekara daya (NYSC), inda yayi aiki a matsayin malamin makaranta, a Government Day Secondary School, dake garin Kiyawa, a jihar Jigawa.

Salisu yana daya daga cikin matasan Nijeriya 100 da aka zaba daga cikin matasa sama da 10,000 da suka samu shiga shirin horas da matasa na kasar Amurka, wato, Mandela Washington Fellowship. na wannan shekarar, shirin da yake zakulo, ya kuma horas da matasa masu gudanar da ayyukan da suke kawo cigaba a fannoni daban-daban a yankunan su, kuma daga sassan daban daban na Afrika. A saboda haka, a halin yanzu, Salisu yana karatu a fannin hada-hadar kasuwanci (Business & Entrepreneurship) ne a Rutgers University, New Brunswick, New Jersey, tare da wasu matasa su 24 daga wasu kasashen na Afrika.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG