Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Minista Solomon Dalung Yayi Tir Da Sallamar Tijani Babangida


Barista Solomon Dalung
Barista Solomon Dalung

Ministan matasa da wasani na Najeriya Barrister Solomom Dalung yayi tir da sauke Tijani Babangida daga matsayin sa na mataimakin na masamman ga kocin Super Eagles Sunday Oliseh.

Ministan ya furta haka ne gabanin wasan da Najeriya zata buga da kungiyar kwallon kafa ta Pharaohs of Eygpt wanda za’a buga a ranar 25, ga watan Maris, a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna.

Ministan ya nuna rashin jindadinsa ga wannan matakin da hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta dauka na sallamar Tijani Babangida duk da namijin kokarin da yayi na gani cewa an samu fahimtan juna tsakanin hukumar da Kocin na kungiyar ta Super Eagles wato Sunday Oliseh, sai kuma aka biyu baya aka salami mataimakinsa na masamman.

Solomon Dalung ya kara da cewa zai yi iya kokarinsa na ganin cewa an samu waraka daga wannan mataki da hukumar ta dauka.

Yace babban matsallar mu a nan Najeriya shine mutane na ji ji da kai amma tilas ne wani lokaci mutun ya hakura ya bada kai buri ya hau domin kasar mu tafi gaban burimu na kashin kan mu.

XS
SM
MD
LG