Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tiger Woods Na Kara Fuskantar Matsanancin Ciwon Baya


Tun a watan Disamba na shekarar 2015, fittaccen dan wasan kwalon “Golf” na duniya Tiger Woods, ya bayyanar da irin hakin da yake ciki na rashin lafiya. A shekarun 2014 da 2015 ne akayi mishi aiki a gadon bayan shi da gwiwa, wanda hakan yasa baya iya fita ko ina. Ya kwashe tsawon watanni yana zaman gida, a cikin wannan yanayin ne yake dan tattakawa da wasu ayyukan motsa jiki don yasamu ya dawoda karfin jikin shi.

Rahotannin na nuni da cewar ya zuwa yanzu, Tiger, yana kara fuskantar matsanancin ciwon baya, wanda hakan na nuni da cewar yana da wuya Tiger, yayi iya dawowa fagen wasa nan kusa. Rashin lafiyan kan iya zama sanadiyar sake zama zakara a fagen kwalon rami “Golf” gare shi. A irin hali da yake ciki ana ganin kamar wannan rashin lafiyar na iya zama wani sanadiyar da zai sa ya bar wasa baki daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG