Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Flamingoes 'Yan Kwallon Mata Na Najeriya Zasu Gwabza Da Afirka Ta Kudu


Kwallon mata
Kwallon mata

‘Yan kungiyar wasan kwallon kafa na mata na Najeriya, na ‘yan kasa da shekaru 17, wato Flamingoes, zasu koma sansanin da ake horas dasu domin fara shirye shiryen gabanin wasan fidda gwani na cin kofin kwallon kafa na duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa za’a gudanar da wasan na cin kofin kwallon kafa na duniya na mata na ‘yan kasa da shekaru 17, ne daga 30, ga watan Satumba zuwa 21, ga Oktoba a kasar Jordan.

‘Yan kungiyar ta Flamingoes sun lallasa Baby Gladiators na Namibia da ci 4 da nema da kuma ci 5 da nema a wasanin da suka buga zagaye na farko da na biyu.

Yanzu zasu kara da Afirka ta kudu a sagayen karshe, ‘yan kungiyar ta Flamingoes basu taba fashin samun gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ba tun da aka fara gasar a shekarar 2008 a kasar New Zealand.

XS
SM
MD
LG